Wani fitaccen malamin addinin Musulunci, Yahuza Haruna Jada, ya kaddamar da sabon littafinsa da ke koyar da ilimin Tajwidi da harshen Turanci don saukaka wa ’yan boko fahimtar dokokin karatun alkur’ani.
An gudanar da bikin kaddamar da littafin mai suna “Reciters’ Guide” wato Jagoran Makaranta Al-kur’ani a babban dakin taro na masallacin kasa da ke Abuja a kwanakin baya.
Mawallafin ya bayyana cewa littafin ya samo asali ne sakamakon bukatar da dalibansa suka nuna na ya rubuta littafin Tajwidi da harshen Turanci.
“dalibaina da nake koyar da su ilimin Tajwidi a masallacin Bilal da ke Kubwa da suke shan wahalar fahimtar littafan Tajwidi da aka rubuta da Larabci su ne suka bukaci na rubuta littafin Tajwidi da harshen Turanci don su sami saukin karantawa.” Inji shi.
Ya ce a cikin littafin ya yi kokarin nuna wa masu karatu ainihin dokokin karatun Al-kur’ani da ruwayar Hafsu.
Ya bayyana cewa ya yi kokarin fadakar da malaman Tajwidi da suke fuskantar kalubalen koyar da shi da harshen Turanci.
Shugaban kwamitin kaddamarwa, Sanata Alkali Abdulkadir Jajere ya yaba wa mawallafin kan abin da ya kira kokarin da ya yi na rubuta littafin.
Ya ce rubuta shi da harshen Turanci zai taimaka wa wadanda ba sa faimtar harshen Larabci su gane dokokin Tajwidi a saukake.
Don a cewarsa ilimin Tajwidi ilimi ne mai sarkakiya sosai wanda yake bukatar nutsuwa kafin mutum ya fahimce shi.
Saboda haka sai ya yi kira ga dalibai da malamai su mallaki littafin don irin alfanun da ke cikinsa.
Shi ma daya daga cikin wadanda suka sayi littafin, Alhaji Haruna Aliyu ya bayyan littafin a matsayin wata kafa da za ta saukaka wa jama’a fahimtar ilimin Tajwidi ba tare da wata matsala ba.
Ya yi kira ga daukacin wadanda suka fanshi littafin su karanta shi tare yin amfani da abin da suka koya wajen karatun Alkur’ani mai tsarki.
An kaddamar da littafin Tajwidi a Abuja
Wani fitaccen malamin addinin Musulunci, Yahuza Haruna Jada, ya kaddamar da sabon littafinsa da ke koyar da ilimin Tajwidi da harshen Turanci don saukaka wa…