✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kaddamar da kungiyar yaran mota ta kasa

Ma’aikatar Sufuri ta Kasa da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Legas sun kaddamar da sabuwar Kungiyar Yaran Mota ta Najeriya wato Bus Conductors Association of Nigeria…

Ma’aikatar Sufuri ta Kasa da hadin gwiwar Gwamnatin Jihar Legas sun kaddamar da sabuwar Kungiyar Yaran Mota ta Najeriya wato Bus Conductors Association of Nigeria (BCAN) tare da sabon yunifom da za su rika sanyawa a lokacin aiki.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi wanda Darakta Uwargida Anthonia Ekpa ta wakilta ya ce daga yanzu ya zama wajibi kowane yaron mota ya yi rajistar zama dan kungiyar BCAN, inda za a ba shi katin shaida yunifom da za rika sanyawa a lokacin da yake kan aiki.

Ma’aikatar ta sufuri za ta sanya sunan wannan kungiya a cikin jerin sunayen masu ruwa da tsaki da take mu’amala da su a kan al’amuran da suka shafi sufuri a kan hanyoyin kasa baki daya. An gudanar da bikin kaddamar da reshen Jihar Legas na kungiyar ne a ranar Alhamis ta makon jiya a Legas, inda a nan gaba za a bude irinsa a sauran jihohin kasa. Sarakuna daga jihohin Kudu Maso Yamma da dukkan masu ruwa da tsaki a kan harkokin sufuri ne suka halarci wajen bikin da aka yi a zauren taro na Sheraton Hotel.

Da take kaddamar da sabuwar kungiyar Uwargida Anthonia ta nemi dukkan ’ya’yan kungiyar su taimaka wa kansu wajen yin kariya daga yawan bata masu suna da ake yi, musamman a kan tayar da jijiyar wuya da fadace-fadace a tsakanin su da fasinjoji. Ta yi kira ga ’ya’yan kungiyar da su yi amfani da wannan dama wajen kare kansu daga zargin satar mutane a motocinsu da ake alakantawa da su.

Babban bako a wajen bikin, Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Ma’aikatan Gwamnati na Kasa (TUC) Kwamared Bobboi Bala Kaigama ya ce: “A kasashen duniya da suka ci gaba, dukkan masu gudanar da kananan ayyuka da sana’o’i suna kafa kungiyoyi da shugabanninsu suke jagorantar kula da al’amuransu baki daya, wanda idan an samu wata matsala to mahukunta sun san irin kungiyar da za su tuntuba domin yin magani. Saboda haka kafa kungiyar BCAN a Najeriya ya zo daidai da lokaci, domin an dade ana zargin motocin bas-bas da gudanar da miyagun ayyuka da suka hada da satar mutane. Yanzu an samu mikakkiyar hanya da za a yi amfani da ita wajen tuntubar kungiya kai tsaye idan wata matsala ta taso.”

Shi ma shugaban kungiyar BCAN na kasa baki daya, Yarima Israel Adeshola cewa ya yi za su tabbatar da cewa an yi aiki da tsare-tsaren kafa kungiya domin duka yaran mota da fasinjoji su ci moriyar kafa ta.