✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kaddamar da Kamus din Hausa zuwa Ingilishi a Kano

Kamusun shi ne irinsa mafi girma da aka wallafa tun a shekarun 1930

An kaddamar da sabon kamus din harshen Hausa zuwa Ingilishi a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) a ranar Asabar.

Littafin, mai shafi 627, wani Bature kuma masani a bangaren harsuna da ke Jihar Indiana ta Amurka, Paul Newman da maidakinsa, Roxana Ma Newman, ne suka wallafa, kuma madaba’ar BUK ce ta buga shi.

Zama matar Adam Zango ya jawo min koma-baya –Amina Rani

Abin da ya sa aka tsere wa matan Hausawa a harkar kasuwanci

Paul dai a shekarar 1972, ya taba zama Darakta na farko a Cibiyar Koyar da Harsunan Najeriya a BUK, lokacin tana Kwalejin Abdullahi Bayero.

A cewar wanda ya yi ta’alikin littafin, kuma Shugaban Hukumar Bunkasa Binciken Ilimi ta Najeriya (NERDC), Farfesa Isma’il Junaidu, kamus din shi ne irinsa mafi girma tun kusan shekarun 1930.

Ya ce an rubuta littafin ne ta hanyar amfani da daidaitacciyar Hausa, yayin da mawallafin littafin shi kuma yana daya daga cikin masu fada a ji a duniya, a bangaren harsunan yankin Tafkin Chadi.

Da yake jawabi, Paul Newman, wanda Shugaban Makarantar Karatun Gaba da Digiri ta BUK, Farfesa Mustapha Ahmad Isa, ya karanta a madadinsa, ya ce kamus din wani muhimmmin cigaba ne a fannin koyarwa da kuma bincike a harshen Hausa.

Ya kuma ce kaddamar da littafin ya zo daidai da lokacin da yake bikin cika shekara 50 da zuwansa Najeriya na farko a 1972.

Paul ya ce, “Shekarun da na shafe a Kano sun taka muhimmiyar rawa wajen nasarar rubuta shi.

“Kamus din zai taimaka wa dalibai da masu binciken harshen Hausa.

“La’akari da yawan asalin Hausawa a duniya da masu amfani da harshen, Hausa, babu tantama na daya daga cikin harsuna mafi muhimmanci a Afirka, kuma daya daga cikin manya a duniya,” inji Paul.

Tun farko da yake nasa jawabin, Shugaban Jami’ar ta Bayero, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya ce kaddamar da littafin ’yar manuniya ce kan irin gudunmawar BUK a bangaren ilimi.

“BUK na daya daga cikin ja-gaba a jerin cibiyoyin ilimi wajen koyar da Hausa a ciki da wajen Najeriya. Mawallafin wannan littafin sananne ne a fannin harsuna.

“Sai da aka kafa kwamitin masana harsuna suka yi nazari sannan suka ba da shawarwari, kuma marubutansa suka karba suka yi murna, kafin a kammala shi,” inji Farfesa Sagir.

Taron dai ya samu halartar Jakadiyar kasar Poland a Najeriya, Joanna Tarnawska da sarakunan Kano da Kazaure da Karaye, da kuma wakilan Gwamnonin Jihohin Kano da Bauchi da Jigawa da Katsina da kuma attajirin nan, Alhaji Aminu Dantata.