An jefe wani ma’aikacin Gidan Talabijin na Kasa (NTA) har lahira a garin Okene na Jihar Kogi.
Wasu da ba a san ko su wane ne ba suka yi wa Mista Chukwu Odiahu, wanda injiniya ne, wannan aika-aika bayan ya tashi daga wurin aikinsa.
- An kai hari gonar Obasanjo an yi gakuwa da ma’aikata
- Sheikh Sani R/Lemu da Umar Sani Fagge sun zama farfesoshi
Da yake tabbatar da faruwa lamarin, wani jami’i a gidan talabijin na NTA da ke Okene ya shaida mana cewa, “Abin takaici ne yadda muka wayi gari yau (Laraba) da labarin rasuwar abokin aikinmu daga sashen injiniya.
“Bayan ya rufe tashar da misalin karfe 10 na dare ranar Talata ne ya bar harabar gidan talabijin din,” inji jami’in da ya nemi a boye sunansa.
Ya ce daga baya ne aka tsinci gawar Injiniya Chukwu bayan wasu da ba a san ko su wane ne ba sun yi masa ruwan duwatsu.
Ya kuma tabbatar mana cewa an tsare ma’aikatan da ke aiki a lokacin da abin ya faru.
Wakilinmu ya gano cewa Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Okene ne ya tsare ma’aikatan da ke aiki a lokacin, domin binciken su a matsayin manyan ababan zarge.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto dai babu tabbacin hakikacin musabbabin rasuwar mutumin.
Wakilinmu ya tuntubi mai magana da yawun ’yan sanda na Jihar Kogi, DSP William Ovye Aya ko zai samu karin bayani, amma bai same shi a waya ba.