Gwamnatin jihar Nasarawa ta dage dokar hana taron ibada, wadda ta kafa da nufin hana yaduwar annobar COVID-19.
Kwamishinan yada labarai da al’adu da yawon bude ido na jihar, Dogo Shammah, ya bayyana haka ranar Talata bayan gwamnan jihar ya gana da masu ruwa da tsaki a Gidan Gwamnati da ke Lafiya, babban birnin jihar.
Mista Shammah ya ce an janye dokar na tsawon makwanni biyu bisa wasu sharudda da dole shugabannin addini da mabiyansu su cika.
- Coronavirus: Za a fitar da almajirai 4,443 daga jihar Nasarawa
- COVID-19: Gwamnatin Nasarawa ta mayar da matafiya 9 Kano
Ya ce sharuddan su ne, dole a sanya takunkumin rufe baki da hanci, samar da man tsaftace hannu da kuma ba da tazara a wuraren ibada.
Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar za ta bibiyi yadda ake bin matakan na kariya da sharuddan da ta gindaya bayan mako biyun, za kuma ta samar da man wanke hannu da na’urar auna zafin jikin mutum a masallatai da coci-coci a fadin jihar.
Bugu da kari Dogo Shammah ya sanar da sassauci a dokar hana hawa babur mai kafa uku (Keke Napep) bisa sharadin za a dinga daukar mutum biyu ne kawai, kuma dole mai jan babur din da fasinjan su sanya takunkumin rufe baki da hanci.
Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshan jihar Nasarawa, Joseph Massin, wanda ya yi magana a madadin shugabannin addini na jihar, yaba wa gwamnatin bisa sassaucin da ta yi, inda ya yi alkawarin za su yi biyayya sau da kafa ga sharuddan da matakan hana yaduwar annobar.
Massin ya yi kira ga daukacin shugabanin addini a jihar da su samar da ruwa tare da ma tsaftace hannu a wuraren ibadar su, su kuma tilasta wa mabiyansu sanya takunkumin rufe fuska.
Wannan mataki da gwamnatin jihar Nasarawa ta dauka na janye dokar hana taro a wuraren ibada ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya ke korafin cewa gwamnatocin jihohi na yin karan tsaye ga kokarin da take yi na dakile yaduwar annobar COVID-19 a kasar.
A ranar 2 ga watam Maris Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya sanya dokar hana taro a wuraren ibada matakin sa na kare yaduwar cutar coronavirus.