✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An janye dokar hana hawa babura a Katsina albarkacin Ramadana

Jama'a suna bukatar su yi walwala a kowane lokaci a watan Ramadana.

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya janye dokar nan da ta haramta hawan babura daga bakin karfe goma na dare a duk fadin jihar.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Alhaji Aminu Isa ya fitar a daren ranar Alhamis.

Babban Darektan Yada Labarai na Fadar Gwamnatin Katsina, ya shaida wa Aminiya cewa an janye dokar da nufin bai wa al’ummar jihar damar gudanar da ayyukansu na ibada a cikin watan azumi na Ramadan, kasancewarsa wata ne wanda jama’a ke da bukatar yin walwala a kowane lokaci.

Ana iya tuna cewa, gwamnatin Jihar Katsina ta sanya dokar hana hawa baburan ne daga bakin karfe goma na dare da a yunkurin da take yi na magance matsalar tsaro da ta addabi jihar, matakin da gwamnatin ta yi ikirarin samun nasara a kai.