✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbi tsohon Fira Ministan Pakistan, Imran Khan

An bindige wanda ya harbi Mista Imran Khan har lahira.

An harbi tsohon fira ministan kasar Pakistan, Imran Khan, a lokacin da yake tsaka da jagorantar wani gangamin siyasa.

Babban Hadimin tsohon fira ministan, Raoof Hasan, ya ce wani dan bindiga ne ya harbi Mista Khan a kafa a wurin zanga-zangar siyasa ranar Alhamis a garin Gujranwala.

Raoof Hasan, ya ce, an harbe mutum da ya harbe Mista Khan har lahira, “Na biyun kuma ya shiga hannun ’yan sanda.”

Sai dai ya bayyana cewa ba a san wanda ya harbi dan bindigar na farko har ya kashe shi ba.

Ya yi zargin cewa, “Wannan yunkuri ne na kashe,” Imran Khan wanda tun ranar Juma’a yake jagorantar gangamin adawa da hukuncin hukumar zaben Pakistan da ta hana shi tsayawa takara a zaben shugaban kasar da ke tafe.

Tsohon fira ministan ya fara tattakin taer da dandazon magoya bayansa ne daga Lahore zuwa Islamabad, babban birnin kasar.

A a yayin tattakin, kullum Imran Khan yakan gabatar da jawabi ga magoya bayansa da ke biye da shi da wadanda ke gefen titi, a yayin da yake tsare bayan wata babbar motar daukar kaya.