✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An harbe masu kutse hudu a Kwalejin Kwastam

An bindige hudu daga cikin miyagun bayan sun yi biris da harbin tsoratarwa

Jami’an Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa sun harbe bata-gari hudu da suka yi yunkurin tsallakawa kwalejin horas da jami’an hukumar da ke Gwagwalada a Birnin Tarayya, Abuja. 

Aminiya ta ruwaito cewar lamarin ya faru ranar Alhamis, bayan jami’an suka yi harbin ban tsoro amma miyagun suka yi kememe wanda hakan ya haddasa kisan.

Majiyarmu a unguwar ta ce da mutanen sun lura jami’an na kwastam sun tsare kofar makarantar sai suka zagaya baya domin su tsallaka katanga.

“Jami’an Kwastam sun yi harbin ban tsoro amma duk da haka mutanen suka yi kokarin tsallakawa. Sai wani jami’i daga ciki ya yi harbin da ya kashe mutum hudu”, inji majiyar.

Ya ce, sauran bata-garin sun ranta a na kare bayan ganin abin da ya faru da ’yan uwansu,.

Gawarwakin mutum hudun kuma an kai su mutuwaren Asibitin Kwararru na Jami’ar Abuja da ke Gwagwalada.

Wani mai makarantar kudi da ke kusa da kwalejin kwastam din Wasiu Shina, ya ce, “Da farko bata-garin sun zo suka lalata motocin mutanen da aka ajiye a gaban kofar makarantata.

“Sun raunata mai gadina suka kuma gudu da babur din direban motar makarantata.

“An gano sunan daya daga cikin wadanda aka harbe, Mohammed Tirmizi, an kuma ce an ba da gawarsa domin yi mata jana’iza”, inji Wasiu.

Kakakin hukumar ta kwastam, Joseph Attah, ya tabbatar da faruwar hakan a hirarsa da Aminiya ta wayar tarho.

A cewarsa, “Bata-garin sun zo Makarantar Horas da Jami’an Kwastam, amma mun kore su”.

Idan ba a manta ba, bata-gari da suka yafa rigar zanga-zangar #EndSARS sun yi ta wawushe rumbunan gwamnati da na ’yan kasuwa daga lokacin da aka fara zanga-zangar kawo yanzu.

Wannan na daga cikin matakan farko da jami’an tsaro suka fara dauka tun lokacin da aka fara kashe su tare da yi musu sace-sace da kone-kone a fadin kasar nan.