Wasu ’yan bindiga sun harbe har lahira Christopher Inalegwu, yaya ga Kwamishinan Yada Labarai, Al’adu da Yawo Bude Ido na Jihar Binuwai.
An dai harbe shi ne lokacin da yake tsaka da aiki a gonarsa, wacce ke kauyen Aku na gundumar Okololo da ke Karamar Hukumar Agatu ta Jihar ranar Litinin.
- Ban san yawan mutanen da na kashe ba – Yaron Bello Turji da ya shiga hannu
- Zan tsaya takarar Shugaban Kasa a zaben 2023 – Tambuwal
Shaidun gani da ido sun ce marigayi Christopher ya gamu da ajalin nasa ne lokacin da maharan suka yi arba da shi a gonarsa, nan take kuma suka bude masa wuta.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar, Michael Inalegwu, ya ce kisan abin takaici ne matuka, musamman kasancewa shi kadai ne shakikin dan uwansa da ke raye.
Sai dai ya lashi takobin cewa ba za su taba daga kafa ga ’yan ta’adda ba a Jihar.
Ya ce bayan an harbi dan uwan nasa an dauki tsawon lokaci kafin a iya kai masa agaji ta hanyar kai shi asibiti, amma aka iske babu likita a wurin.
Ya ce sakamakon raunukan da ya samu, an garzaya da shi zuwa wani asibitin na daban, inda ya karasa mutuwa ’yan mintuna bayan isa can.
Kwamishinan ya ba da tabbacin cewa Gwamnatin Jihar za ta yi duk mai yiwuwa wajen aikewa da jami’an tsaro zuwa Gwer ta Yamma da kuma Agatu, wadanda ake yawan kai musu hare-hare.
Da wakilinmu ya tuntubi Kakakin ’Yan Sandan Jihar, SP Catherine Anene, ta ce ba ta kai ga samun rahoton kisan ba tukunna.