Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Filato ta tabbatar da kisan mai bai wa Gwamnan Jihar Binuwai Samuel Ortom shawara kan harkokin tsaro, Christopher Dega.
An kashe Christopher Dega, wanda tsohon Mataimakin Sufeto Janar ma ’Yan Sanda ne a wani gidan abinci da ke Bukuru, a yankin Karamar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar ta Filato.
- Zan ba wa masu tada tarzoma a Najeriya mamaki — Buhari
- Kamfanoni 75 sun nuna sha’awar sayen tituna 12 daga Gwamnatin Tarayya
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, ASP Ubah Gabriel ya shaida wa ’yan jarida a Jos cewa tuni aka kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da aikata kisan.
A cewar Rundunar, bincike ya nuna cewa an yi hakon marigayin ne har zuwa gidan abincin da lamarin ya faru.
“Rundunar ’yan sanda ta samu mummunan labarin kisan Mataimakin Sufeta Janar Christopher Dega (mai ritaya).
“Wadansu ’yan bindiga ne suka kashe shi ranar Litinin da misalin 8:30 na dare a gidan cin abincin da ke Bukuru, a Jos.
“Ya shigo Jos ne daga Makurdi da misalin karfe 7:30 na dare a wannan ranar.
“An kama wadansu da ake zargi da hannu a kisan, sannan ana ci gaba da gudanar da bincike,” inji shi.