✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta zuwa da kare wajen zabe

Rundunar ta ce zuwa wurin zabe da karnuka ya saba wa dokar zabe ta 2022.

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta gargadi ’yan kasar gane da zuwa da karnuka da sauran dabbobi wajen kada kuri’a a zaben gwamnoni da na ’yan majalisar dokokin jiha da za a yi ranar Asabar.

Wannan dai na zuwa ne bayan da wasu masu kada kuri’a suka yi korafin an kai musu hari da dabbobi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan da ya gabata.

Sai dai a wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Talata, ta hori jama’a da su daina kai karnuka da sauran dabbobi zuwa rumfunan zabe.

“Ya zama wajibi Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta wayar da kan ’yan Najeriya game da zuwa da dabbobi musamman karnuka rumfunan zabe, domin kuwa hakan ya saba wa Dokar Zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima.

“Sashe na 126 (1) na Dokar Zabe ta 2022, ya bayyana karara cewa yin hakan da masu zabe suka yi ya saba doka kuma za a hukunta su.

“Ana iya amfani da karnuka a matsayin makami kuma masu kula da su za su iya amfani da su don tsoratarwa ko musgunawa ga masu zabe.

“Yana da kyau mutane su daina zuwa wurin yin zabe da karnuka ko kuma wasu nau’in dabobbi domin hakan ya saba da doka.

“Saboda haka Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta gargadi wadanda ke da niyyar kai dabbobinsu, musamman karnuka rumfunan zabe, da su guji saba wa Dokar Zabe ta 2022 da sauran wasu dokoki,” in ji sanarwar.