✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta zancen dare a Jigawa

An haramta zancen dare a tsakanin saurayi da budurwa a Karamar Hukumar Kirikasamma da ke Jihar Jigawa a wani yunkuri na magance yawaitar lalata ’yan…

An haramta zancen dare a tsakanin saurayi da budurwa a Karamar Hukumar Kirikasamma da ke Jihar Jigawa a wani yunkuri na magance yawaitar lalata ’yan matan.

Majalisar Kansilolin Karamar Hukumar ce ta yi wannan doka  daga bisani Shugaban Karamar Hukumar ya sa wa dokar hannu, inda aka gudanar da kwarya-kwaryar biki, kamar yadda Jami’in Watsa lLbarai na Karamar Hukumar, Malam Sanusi Doro ya shaida wa BBC.

Jami’in ya bayyana cewa bisa tanadin sabuwar dokar, idan aka kama saurayi da budurwa suna zance da dare, “Za a yanke musu hukuncin zaman gidan yari na wata shida, ko kuma tarar Naira dubu 50.”

Karamar Hukumar ta ce daya daga cikin dalilan da suka sa aka dauki wannan mataki shi ne batun “Yawaitar juna biyu da ake samu kafin yin aure.”

Malam Sanusi ya kara da cewa: “Duk wanda aka kama yana hira da budurwa ko a manyan garuruwa ko kanana ko a rugagen Fulani, za a gabatar da shi a gaban kotu, kuma zai biya tarar Naira dubu 50, ko kuma ya yi wata shida a gidan kurkuku.’’

Ya ce yanzu haka akwai wanda ya kawo shawarar a hana kidan dije (DJ) da samari da ’yan mata ke rawa tare a lokacin biki.