An umarci bankunan kasar Zimbabwe da su daina ba da rancen kudade ga masu neman bashi daga kan ma’aikatun gwamnati har zuwa masu zaman kansu.
Shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe ne ya bayyana hakan yana mai cewa dokar ta soma aiki nan take.
- Firaministan Sri Lanka ya yi murabus
- ‘Bai kamata jirgin kasan Abuja-Kaduna ya dawo aiki ba a kubutar da ’yan uwanmu ba’
An dauki matakin ne domin rage yawan yaduwa kudaden kasar da zimmar shawo kan karayewar da darajarsa ke yi.
Dalar Zimbabwe ta rage daraja da kusan kashi 50 cikin 100 a wannan shekara, yanayin da ya sa ta kasance kudin da a yanzu a Afirka ya fi fuskantar koma-baya.
A wani jawabi ta kafar talabijin din kasar, Shugaba Mnangagwa ya sanar da wasu matakai, ciki har da kara kudin haraji kan hada-hadar kudaden ketare tsakanin bankuna, da karbar takardar kudi a banki.