✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta sayar da dabobbi a kasuwannin Katsina

Gwamnatin Katsina ta dauki matakin ne don tsaurara matakan tsaro a fadin jihar.

Gwamnatin Jihar Katsina ta haramta zirga-zirgar ababen hawa a hanyar da ta tashi daga Jibiya zuwa Gurbin Baure har sai abin da hali ya yi.

Ta kuma haramta wa motocin haya bin hanyar Kankara zuwa Sheme, tare da umartar wadanda dokar hana bin hanyoyin ta shafa da su koma bin hanyar Funtuwa.

Dokar da ta fara aiki ranar Talata 31 ga Agusta, 2021, domin tabbatar da tsaro a Jihar Katsina, wadda ’yan bindiga suka addaba, ta haramta sayar da dabbobi a kasuwannin kananan hukumomi 14 na jihar ko daukar dabbobi a manyan motoci daga ko’ina a cikin jihar zuwa wajenta.

Kasuwannin dabbobin da dokar ta shafa su ne kasuwar Jibiya da Batsari da Safana da Charanchi da Mai’adua da Malumfashi da Kafur da Sabuwa da Kankara da Faskari da Baure da Danmusa da Dutsinma da  kuma kasuwar Kaita.

Gwamnatin ta kuma sanya haramci a kan manyan motoci da ke daukar itace daga dazukan da ke fadin Jihar.

Ta hana daukar fiye da mutum fiye da uku a kan mota ’yar kurkura ko daukar mutum fiye da uku a kan babur a fadin jihar ta kuma haramta sayar da tsofaffin babura a kasuwar Charanchi.

Gwamnatin Jihar Katsina ta ta jaddada haramcin zirga-zirgar babura daga karfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe da kuma karfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a kananan hukumomin da matsalar rashin tsaron tafi addaba.

Ta ce har yanzu haramcin sayar da man fetur a cikin Jarka na nan na aiki, kuma gidajen mai biyu kadai ne gwamnati ta amince su rika sayarwa a kananan hukumomin da matsalar rashin tsaro tafi addaba.

An kuma haramta wa gidajen mai sayar wa mutum daya man fetur da ya wuce na N5,000 a kananan hukumomi da matsalar tsaron ta fi kamari.

Kananan hukumomin su ne Jibiya da Batsari da Safana da Musawa da Matazu da Kafur da Sabuwa da Kankara da Faskari da Danmusa da Kurfi da Dutsinma da Danja.

Amma an amince wa ma’aikatan lafiya da jami’an tsaro da ’yan jarida su yi amfani da babura ko Keke Napep a yankunan da dokar ta shafa.