✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An haramta nuna fina-finan garkuwa da mutane a Kano

Fina-finan ta’ammali da miyagun kwayoyi ma an haramta su a Kano.

Gwamnatin Kano ta haramta nunawa ko sayar da fina-finai da ke tallata garkuwa mutane ko kwacen waya ko ta’ammali da miyagun kwayoyi a fadin jihar.

Sabuwar dokar wani yunkuri ne na gwamnatin jihar domin magance matsalolin uku da ke ci wa Jihar Kano tuwo a kwarya, duk da kokarin da hukumomin tsaro ke yi domin shawo kansu.

Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta sanar cewa “Daga yanzu an haramta fina-finai da ke nuna garkuwa da mutane ko ta’ammali da miyagun kwayoyi ko kwacen waya, matsalolin da ke illata al’ummar Jihar Kano.”

Shugaban hukumar, Isma’il  Naabba Afakallah, ya ce manufar haramta nau’ikan fina-finan ita ce kawar da yiwuwar matasan Kano su koyi aikata miyagun laifuka a dalilin kallon fim.

“Ba kowane matashi ne ke da hankalin fahimtar sakon da ke cikin kirkirarrun fina-finan ba; Wani zai iya dauka da gaske ne, ya je ya aikata irin abin da ya gani a ciki; Saboda haka ya zama wajibi mu dauki mataki tun ba mu makara ba”, inji Afakallah.

A yayin da matsalar garkuwa da mutane ke addabar yankin Arewa maso Yammacin Najeriya, lamarin ya yi kamari a jihohin Kaduna da Katsina, wadanda ke makwabtaka da Jihar Kano.

– Matsalolin sun dabaibaye Kano

Akan kuma samu daidaikun rahotannin garkuwa da mutane a Jihar Kano, sannan an sha kama wadansu da suka yi garkuwa da mutane a wasu wuraren sun mayar Kano maboyarsu.

Kano ta kuma yi kaurin suna wajen yawan masu ta’ammali da miyagun kwayoyi, maza da mata, masu kowane irin shekaru.

Ko a kwanakin baya, Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Muhammad Buba Marwa, ya ce sama da mutum milyan biyu ne ke shan miyagun kwayoyi a Jihar Kano.

Masu kwacen waya kuma, wadanda galibi masu shaye-shaye ne, sun kashe mutane da dama baya ga wadanda duka daba wa makami a Kano, inda matsalar ta yi kamari.

Idan ba a manta ba, ko a cikin watan azumin Ramadan, Aminiya ta kawo rahoton yadda masu kwacen waya suka yi ta ritsa mutane a hanyar zuwa sallar tahajjud, suna kwace musu dukiyoyinsu.

Wani bincike da Aminiya ta gudanar ya gano yadda masu kwacen wayar ke hada baki da masu damfara ta intanet, wadanda ke amfani da layukan wayoyin da aka kwace su wawure kudaden masu layukan wayar a banki.