✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hana mata sanya hijabi a Diffa

A shekaranjiya Laraba ne aka sanar da dokar hana sa hijabi ga mata a Jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar, tun daga yanzu har zuwa wani…

A shekaranjiya Laraba ne aka sanar da dokar hana sa hijabi ga mata a Jihar Diffa ta Jamhuriyar Nijar, tun daga yanzu har zuwa wani dan lokaci, kamar yadda BBC ta bayyana.

Hukumomin sun ce an dauki matakin ne da nufin magance matsalar hare-haren Kunar baKin-wake da ake fuskanta, musamman yadda a kan yi amfani da wasu mata sanye da Hijabi.
Malamai a jihar sun ce sun gamsu da dokar bisa la’akari da yanayin dar-dar da ake ciki a fadin jihar.
Ko a baya ma gwamnatin jihar ta Diffa ta yi hani da sanya burka ga mata sakamakon karuwar hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram a sassan jihar.
Jihar Diffa dai na daya daga cikin jihohin da ‘yan Kungiyar Boko Haram suka mayar karkatacciyar kuka a jamhuriyar Nijar.