✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hana cin kasuwar dare a Adamawa

A shekaranjiya Laraba ne Gwamnatin Jihar Adamawa ta haramta cin kasuwanni da kuma dafifin jama’a da daddare domin kauce wa hare-haren bama-bamai na masu tayar…

A shekaranjiya Laraba ne Gwamnatin Jihar Adamawa ta haramta cin kasuwanni da kuma dafifin jama’a da daddare domin kauce wa hare-haren bama-bamai na masu tayar da kayar baya.
Wannan matakin ya biyo bayan wani hari ne da aka kai ranar Talata da dare a wata kasuwa a Yola babban birnin jihar.
Hukumomi sun ce wani mutum ne ya yaudari jama’a, ya tara su, yana raba masu kudi, sai kwatsam ya tayar da bam, wadda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 34 da kuma jikkata wasu guda 86.
Kwamishinan watsa labaran Jihar Adamawa, Alhaji Ahmad Sajo, ya shaida wa wakilin BBC cewa an yanke shawarar haramta bude kasuwannin da dare ne, a yayin taron Majalisar Tsaron jihar shekaranjiya Laraba.
Har ila yau, a shekaranjiya ne wasu mata biyu ’yan kunar bakin wake suka kai harin bam a kasuwar sayar da wayoyin hannu a Farm Centre da ke birnin Kano. Harin ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 15 da kuma jikkata wasu fiye da 50.