Jamhuriyar Benin ta shiga jerin kasashen Afrika da suka yi dokar halasta zubar da ciki, bayan tafka muhawara mai zafi a majalisar dokokin kasar a ranar Laraba.
A baya majalisar dokokin kasar ta yi dokar haramta zubar da ciki, sai dai idan fyade aka yi wa mace, ko kuma saboda rashin lafiya da ke iya salwantar da rayuwar mai juna biyun ko kuma cikin da take dauke da shi.
- Najeriya A Yau: Harin Jirgin Kasa ya ja wa Najeriya asarar N25m a kullum
- Trump zai bude sabon shafin sada zumunta na kashin kansa
Bayan tafka muhawara mai zafi kan kudurin dokar halasta zubar da cikin, wasu daga cikin ’yan majalisar sun ki amince, amma duk da haka kudurin ya samu damar tsallakawa sannan ya zama doka a yanzu.
Sabuwar dokar ta ayyana cewa za a iya zubar da cikin ne idan yana wata ukun farko, idan zai jawo nakasu ga harkar ilimi, aiki, yanayi ko kuma lafiyar macen da ke dauke da shi.
Mata akalla 200 ne ke mutuwa duk shekara a dalilin zubar da ciki, kamar yadda Ministan Lafiya na kasar, Benjamin Hounkpatin, ya bayyana a ranar Alhamis cikin wata sanarwa.
Wasu daga cikin kasashen Afrika da suka hada da Congo-Brazzaville, Congo, Djibouti, Masar, Guinea-Bissau da kasar Senegal, dukkaninsu sun haramta zubar da ciki.