Masu hakar ma’adinai a kasar Angola sun hako wani lu’ulu’u da babu kamarsa a yanzu a duniya, wanda rabon da a samu kamarsa tun shekara 300 da suka wuce.
An hako wannan nau’in dutse mai daraja ne a wata mahakar ma’adinai ta Lulo Alluvia da ke Arewa maso Gabashin kasar Angola a ranar Laraba.
Lu’ulu’un mai launin ja-ja ya kai nauyin karat 170, an kuma sa masa suna ‘Lulo pink Rose’ a cewar wani rahoto na BBC.
A wata sanarwa da ya fitar, Ministan Albrkatun Kasar Angola, Diamantino Azevedo, ya ce, “Katari da wannan dutse mai daraja na nuna irin albarkatun da kasar ke da shi a Afirka”.
A baya, an sayar da kwatankwatacin wannan dutse mai daraja da tsadar gaske.
A shekarar 2017 an sayar da wani lu’ulu’u mai nauyin karat 59 kan kudi Dala miliyan 71.2 wanda ake ganin ya fi kowanne tsada a duniya har yanzu.