Ana dai tuhumar matashin ne da laifuka biyu, duk da cewa ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi.
- Buhari ya nadawa hukumar kula da gidajen gyaran hali da ta NSCDC sabbin shugabanni
- Ba lallai ta’addanci ya kare nan da shekaru 20 masu zuwa ba – Buratai
Dan sanda mai shigar da kara a gaban kotu, Kayode Adeoye, ya shaidawa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar uku ga watan Febarairun 2021 a unguwar Owoeba dake Karamar Hukumar Oshogbo.
Yace wanda ake tuhumar ya ranci kudaden a hannun wani mai suna Obisesan Olalekan, bisa alkawarin zai dawo masa da kudadensa amma ya gaza yin hakan.
Dan sanda ya ci gaba da cewa, aikata wannan laifin ya saba da sassa na 419 da 383 na Kundin Dokoki na Jihar Osun.
Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai shari’a Isola Omisade, ya bayar da belin wanda ake tuhuma kan kudi N500,000, da kawo mutane biyu da za su tsaya masa.
Alkalin ya kuma ce cikin mutane biyun da za su tsaya masa, dole daya daga ciki ya kasance ma’aikacin gwamnati, dayan kuma ya kasance dan uwansa na jini.
Dagan an sai ya dage zaman kotun zuwa ranar 22 ga watan Maris don ci gaba da sauraron karar.