An gurfanar da ‘yan kasar China su biyu da ake zarginsu da yunkurin bayar da rashawa ta Naira miliyan 100 ga shugaban Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati a Najeriya (EFCC) na shiyyar Sakkwato a gaban babbar kotun jiha ranar Juma’a.
Wadanda ake zargin sun hada da: Meng Wei Kun da Xu Kuoi ana tsare da su ne tun a ranar Jumu’ar data gabata kan cin amanar kasa da wulakanta aikin gwamnati, bayan an karanta masu laifin da ake tuhumarsu ba su amince da shi ba.
Bayan sun gabatar da bukatarsu ga Alkali Muhammad Sifawa lokacin da yake sauraren Shari’ar ya dage sauraren karar har zuwa ranar 15 ga watan Yunin 2020 don ci gaba da sauraren karar.
- EFCC ta gurfanar da Kabiru Tanimu Turaki a gaban kotu
- Orji Uzor Kalu: Za mu koma kotu nan take –EFCC
Alkali ya bayar da umarnin hukumar EFCC ta ci gaba da tsare wadanda ake zargin har sai an saurari korafinsu na bukatar a bayar da su beli a ranar 18 ga watan Mayu.
Rahoton Aminiya ya bada labarin yanda shugaban yankin na Sakkwato ya ki karbar kudin rashawa da ‘yan Chana suka ba shi a farko na miliyan 50 somin tabi kafin cika sauran miliyan 100.