✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gurfanar da wanda ake zargi da satar Baibul a kotu

Kotu ta ba da belin sa a kan kudi N200,000 da shaidu guda biyu

An gurfanar da wani mutum a gaban Kotun Majestare da ke Jihar Legas, bisa zargin sa da sace littafin Baibul guda hudu wanda a kiyasce kudinsu ya kai Naira dubu 72,230.

Wanda ake zargin ma’aikaci ne a wani shagon zamani inda a nan ake tuhumar sa da satar litattafan na Baibul.

Mai gabatar da kara, Sufeta Felicia Okwori, ta shaida wa kotu cewa mai kare kansa ya aikata laifuffukan da ake tuhumarsa ne a ranar 4 ga Disamba, 2021 da kuma 3 ga Yuni, 2022 a yankin Ikeja.

Ta ce an gano laifukan da mutumin ya aikata ne da taimakon kyamarar tsaro ta CCTV, inda ya shiga shagon a lokuta mabambanta ya kwashi littafin Baibul hudu wanda darajarsu ta kai N72,230.

A cewarta, laifukan sun saba wa sassa na 287 da 411 na dokokin manyan laifuka na Jihar Legas.

Sai dai wanda ake zargi ya musa tuhumar da ake yi masa.

Daga nan, alkalin kotun, Misis H. B Mogaji, ta ba da belin sa a kan kudi N200,000 da shaidu guda biyu.

Alkali Mogaji ta dage ci gaba da shari’ar ya zuwa 25 ga Nuwamba, 2022.