Sojoji 68, ciki har da hafsohi za su gurfanar a gaban kotun soja kan aikata laifi a yaki da ’yan bindiga.
Da yake kaddamar da kotun, Babban Kwamandan Runduna ta 8 da ke Sakkwato, Manjo-Janar Uwem Bassey, ya ce hafsohin da lamarin ya shafa sun aikata laifuffukan da ake tuhumar su ne yayin da suke aiki da Rundunar Hadarin Daji, mai yaki da ’yan bindiga a jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Katsina.
- Sankarau ta kashe mutum 56 a Najeriya —NCDC
- Gasar Kofin Duniya: Qatar ta rage lokacin aiki da makarantu
Bassey ya yi kira ga mambobin kotun da su bi doka sau da kafa da adalci yayin zaman shari’a, yana mai cewa , “Dole kotu ta tabbatar da adalci ta hanyar auna dukkanin hujjojin da za a gabatar mata.
“Domin kuwa wadanda ke za su fuskanci shari’ar jami’ai ne kuma dole a kula su da matarbawa da kuma adalci.”
Daga nan, ya ba da tabbacin kotun za ta yi aikin da aka dora mata daidai da doka kamar yadda yake a cikin Kundin Tsarin Mulki na 1999 wanda aka yi wa kwaskwarima.
Shi ma lauya mai kare wadanda ake tuhuma, Barista Godwin Uwadiae, ya ce yana da kwarin gwiwa kotun za ta yi adalci ga wadanda ake zargin.