An gurfanar da wani matashi a gaban wata Kotun Majistare da ke Ile-Ife kan zargin karbar wayar salula ta sata.
Dan sanda mai shigar da kara, ASP Sunday Osanyintuyi, ya shaida wa kotun cewa, mutumin da ake tuhumar ya aikata laifin ranar 18, ga watan Janairun 2021 da misalin karfe 6:30 na yamma a yankin Adejohun Compound dake Ilare, Ile-Ife.
- Shugaban Kasar Syria da matarsa sun kamu da COVID-19
- Fallasa a Katsina: Yadda Mahadi ya gurfana a gaban kotu
Osanyintuyi, ya ce mutumin ya karbi tsabar kudi N30,000 da wayar kirar Tecno Camon15, duk da yana da masaniyar cewa wayar ta sata ce.
Dan sandan ya ce, laifin ya sabawa sashe na 427 na dokokin hukunta manyan laifuka ta Jihar Osun na shekarar 2002.
Amma wanda ake tuhumar ya ce sam ba shi da hannu a abun da ake tuhumarsa da aikatawa.
Alkalin Kotun, A. A. Adebayo, ya bayar da belin wanda ake tuhumar kan kudi N50,000 da kawo mutumi daya da zai tsaya masa.