Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Taraba ta gurfanar da wasu mutum 40 a kotu kan laifin wawaso a ma’ajiyar gwamnati da ta ’yan kasuwa a garin Jalingo.
Kakakin Rundunar Yan Sanda Jihar Taraba, DSP David Misal ya shaida wa Aminiya cewa an kama mutanen ne a sassan garin Jalingo da kayayyakin da suka sace a wuraren ajiyar kayan gwamnati da na sauran jama’a a wurinsu.
DSP David Misal ya da bayyana cewa a na tuhumar wadanda aka gurfanar da laifukan sace kayayyakin gwamnati da na sauran jama’a tare da tayar da hargitsi da kuma tayar da zaune tsaye.
Ya ce rundunar ta kuma samu nasarar gano kayayyakin da aka sace masu yawa yayin da ‘yan sanda ke farautar wasu gungun masu aikata laifuka wadanda sune a gaba-gaba wajen fasa wuraren ajiya na gwamnati da na sauran jama’a tare da sace kayayyakin na miliyoyin nairori a garin Jalingo da Wukari.
A wani labari kuma kwamitin da gwamnatin Jihar ta kaddamar domin kwato kayayyakin gwamnati da na sauran jama’a da bata-gari suka wawushe ya fara zamansa a garin Jalingo.