Gwamman mutane masu alaka da wata kungiyar masu tsatsauran ra’ayi a Faransa sun gurfana a gaban kotu, bayan an zarge su da kitsa kashe shugaba Emmanuel Macron.
Masu gabatar da kara sun ce ‘yan kungiyar Barjols su 13 sun hada baki wajen kitsa juyin mulki, wanda ya kunshi shirin kai wa shugaba Macron hari a shekarar 2018.
- Ministan Cikin Gidan Ukraine da wasu mutum 14 sun mutu a hatsarin jirgin sama
- Mun kashe $1bn wajen kwato yankunan da ’yan ta’adda suka mamaye – Buhari
Masu gabatar da karar sun ce wadanda ake zargin sun kuma shirya kashe bakin-haure tare da kai hare-hare kan masallatai.
An tuhume su da hada baki don aikata ta’addanci, wadda aka tanadi hukuncin daurin shekara 10 a kai.
Sai dai babu wani abin da wadanda ake zargin suka aiwatar daga cikin laifukan da ake zarginsu da su, abin da ya sa lauyarsu, Lucile Collot, ke cewa an gurfanar da su ne bisa tunani mara makama.
A 2018, Hukumar Tattara Bayan Sirri ta Faransa ta samu bayanan da ke nuni cewa, masu tsatsauran ra’ayi a yankin kasar mai tsaunuka na shirin kai wa shugaba Macron hari a yayin bikin tunawa da gwarazan yakin duniya a watan Nuwamban 2022.
Daga nan ne suka fara gudanar da bincike a ranar 31 ga watan Oktoba, har wadanda ake zagin suka shiga komarsu.