✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gurfanar da matashin da aka kama da katinan zabe 29 a gaban kotun Kano

"Wanda ake zargin ya ce Ganduje ne ya sa shi tattara katinan"

An gurfanar da wani matashi mai suna Tasiu Abdu Hayin Gado a gaban kotun Majistare Mai lamba 14, bisa kunshin tuhumar mallakar katin zabe har guda 29 ba bisa ka’ida ba.

Mai gabatar da kara kuma lauyar gwamnati sannan mai wakiltar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Barista Badiha Lawan, ta shaida wa kotun cewa an kama matashin ne da katunan zabe masu yawa da hakan ke nuni da cewa ba mallakinsa ba ne.

Bayan karanto masa takardar karar, wanda ake zargi ya musanta laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.

Barista Badiha Lawan ta roki kotun ta ba su wata rana domin su gabatar da shaidarsu.

A nan ne shi kuma Lauyan wanda ake tuhuma, Barista Isa Baba ya roki a ba su beli rokon da kotun ta ki amincewa da shi.

Kotun, wacce ke karkashin jagorancin Mai Shari’a Mustafah Saad Datti, ta sanya ranar 30 ga Janairu, 2023 domin duba yiwuwar ba da belin wanda ake tuhunar ko akasin haka.

Sai dai bayan fitowa daga kotun, Aminiya ta zanta da lauyan masu kara, Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzurci, wanda ya ce tun a lokacin binciken ’yan sanda sun ce wanda ake zargi ya ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje shi ne ya sanya shi tattara katinan har guda 29.