An gurfanar da wani mutum mai shekaru 33 a gaban wata Kotun Majistare dake Ado-Ekiti kan zargin fasa shago da satar kayar salula.
Mutumin wanda aka sakaya Adereshinsa, ana tuhumar sa ne da laifuka uku da suka hada da balle shago da barnata dukiya da kuma sata.
- Abin da Sarkin Kano ya fada wa gwamnati kan kula da matasa
- Kotu ta tsare ‘barayin kananan yara’ a gidan yari
Dan sanda mai shigar da kara, Insp. Oriyomi Akinwale, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar tare da wasu mutum bakwai da suke gudun buya sun balle shagon wani mutum mai suna Lawal Oluwaseyi, suka sace masa kayan wayar salula da kimarsu ta kai Naira miliyan daya da dubu dari daya.
Ya ce mutumin da abokan ta’asar tasa sun lalata silin din shagon samfurin P.O.P da kimar kudinsa ta kai N100,000; suka balla asusun ajiya na zamani na N500,000; sun kuma lalata wayoyin lantarki na N100,000 da kuma P.V.C da kudinsa ya kai N25,000.
Sun kuma lalata kofa da kudinta ya kai N10,000 da kuma injin janareto na N152,000, wadanda jimmilarsu ta kai N887,000.
Akinwale ya ce hakan da suka aikata a ranar 2 ga watan Fabrairu, 2021 da misalin karfe 2:00 na dare a unguwar Ijigbo da ke garin Ado-Ekiti laifi ne karkarshin sashe na 413 da 390(9) da kuma 451 na kundin hukunta manyan laifuka na Jihar Ekiti na 2012.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta abin da ake tuhumar sa da aikatawa.
Alkalin Kotun, Misis Adefumike Anoma, ta bayar da belin wanda ake tuhumar kan N50,000 tare da kawo mutum daya da zai tsaya masa, sannan ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 12, ga watan Maris.