✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gurfanar da masu shirya sharholiyar tsiraici a Kaduna

An gurfanar da masu ginin da aka shirya gudanar da sharholiyar tsiraici a Kaduna, bayan Gwamnatin Jihar ta rushe ginin. Mutum biyar din sun hada…

An gurfanar da masu ginin da aka shirya gudanar da sharholiyar tsiraici a Kaduna, bayan Gwamnatin Jihar ta rushe ginin.

Mutum biyar din sun hada da kakakin jam’iyyar PDP a jihar, wanda matarsa ce mai Asher Restaurant and Lounge, inda aka shirya sheka ayar.

Hukumar Kula da Tsara Birane ta Jihar Kaduna (KASUPDA) ta rushe ginin da aka shirya yin sharholiyar ne saboda yunkurin zinace-zinace da kuma saba dokar kariyar COVID-19 na rufe wuraren casu.

A narar 31 ga Disamba 2020, KASUPDA, bisa umarnin Gwamna Nasir El-Rufai, ta ruguje ginin bayan bullar takardun tallar casun batsar a shafukan sada zumunta.

Da farko hukumar ta ce ta rushe wurin ne saboda sharholiyar da aka shirya yi a ciki, daga bisani kuma ta fitar da sanarwa cewa ginin ba shi da takardun mallaka balantana na izinin ginawa daga gwamantin jihar.

Kazafi aka yi musu

Mai gidan na Asher Restaurant and Lounge ta karyata ikirarin ’yan sanda na cewa sun kama wadanda suka shirya casun tsiraicin.

Ta ce biyu daga cikin mutanen da ’yan sanda suka kama ma’aikatanta ne, ta kuma zargi ’yan sanda da karbar N100,000 daga wurinta kafin su bayar da belin metanen.

Aisha ta kara da cewa ’yan sandan sun kuma karbi N20,000 daga wurinta domin bibiyar lambar wayar da aka sanya a takardar gayyatar casun.

Matar ta ce rusau din da aka yi, ya sa ta yi barin ciki wata daya, da kuma asarar dukiya ta miliyan N32.

Aminiya ba ta samu jin ta bakin ’yan sanda game da zargin da matar ta yi wa jami’ansu ba.

Tuhumar da ake yi

A ranar Laraba aka gurfanar da wadanda ake zargi da shirya casun tsiraici da jima’i da kuma gayyata zuwa gare shi a gaban Kotun Majistare ta Gabasawa bisa zargin karya dokar COVID-19 da kuma fitsara.

Ana kuma zarge su da karya dokar kullen jihar, hadin baki don aikata laifi, da kuma yunkurin tayar a hankalin al’umma, badala da zina.

’Yan sanda sun ce sun shaida wa kotun cewa sun kama mutanen ne a Asher Restaurant and Lounge, inda sama da mutum 50 maza da mata suka taru suna rawa kusan tsirara ba tare da sanya takunkumi ba.

Suka ce da ganin ’yan sanda, sai mutanen suka rika haura katanga suna tserewa; sai dai wadanda ake tuhuma sun musanta zargin.

Kotun ta bayar da belin kowannensu a kan N100,000 da kuma mai tsaya masa, wanda wajibi ne ya mallaki gida a Kaduna, sannan ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 20 ga watan Janairun 2021.