An gurfanar da wani magidanci a gaban wata Kotun Majistare mai zamanta a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, kan zargin daba wa surukinsa kwalba a kai.
Lauyan mai gabatar da kara, Sufeta Evelyn Motim, ta fada wa kotun cewa, mai kare kansa ya aikata laifin ne ranar 30 ga watan Oktoba a yankin Abule Ijaye da ke jihar.
- PDP ta kori tsohon dan takararta na Gwamna a Ogun daga jam’iyyar
- ‘Yan bindiga sun yi wa Hakimi yankan rago a Kebbi
Ta ce wanda ake zargin ya daba wa mahaifin matarsa wata fasasshiyar kwalba a kai.
Ta ce surukin ya gamu da iftila’in ne bayan da aka gayyato shi don ya zo ya sasanta matsalar aure, daga nan wanda ake zargi ya hada baki da wasu suka lakada wa surukin duka.
Lauyar ta ce wannan laifi ne da ya saba wa sassa na 516 da 355 na Kundin Dokokin Manyan Laifuka na Jihar Ogun na 2006.
Alkalin kotun ya ba da umarnin a kai wanda ake zargin kurkuku a ajiye zuwa lokacin da zai biya kudin beli N50,000 da aka yanka masa da kuma shaida daya.
Daga nan, ya dage shari’ar zuwa 23 ga Nuwamba don yanke hukunci.
(NAN)