✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da likitocin bogi 2 a gaban kotun Legas

Kotun ta dage sauraren karar har zuwa ranar 17 ga watan Janairu, 2023.

Wasu mutum biyu sun gurfanar a gaban Kotun Majistare da ke zamanta a yankin Ejigbo na Jihar Legas, kan zarginsu da mallakar shaidar zama likita ta bogi.

’Yan sanda su gurfanar da Franklin Poroye da Adedayo Ayodele a gaban kotun, bisa zarginsu da hadin baki, cuta, da kuma zamba.

Dan sanda mai shigar da kara, ASP Benedict Aigbokhan, ya ce wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar daya ga watan Janairun 2022, a asibitin Jumoke da ke Orisunbare Shasha a Legas.

A cewarsa, mutanen biyu sun yi amfani da shaidar likita ta bogi wajen neman aiki a asibitin, wanda ya ce hakan ya saba wa doka.

Ya ce wadanda ake zargin sun sani cewar hakan na iya cutar da marasa lafiya a asibitin.

Aigbokhan, ya ce laifin ya saba wa tanade-tanaden sassa na 166 da na 365 da na 380 da kuma na 411 na kundin laifuka na 2015 na Jihar Legas.

Alkalin kotun, Mai Shari’a K. A. Ariyo, ta bayar da belin kowanensu a kan kudi Naira 500,000 tare da gabatar da wadanda za su tsaya musu.

Alkalin ta ce dole ne wadanda za su tsaya musu, su kasance masu aikin yi sannan daya cikinsu ya kasance dan uwa shakiki na kowane daga cikinsu.

Kotun ta ce dole ne wadanda za su tsaya musu su gabatar da shaidar biyan haraji ta Gwamnatin Jihar Legas.

Daga nan sai ta dage sauraren karar har zuwa ranar 17 ga watan Janairun 2023 mai zuwa.