✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da farfesa a gaban kotu bisa zargin magudin zabe

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) reshen jihar Akwa Ibom ta gurfanar da Farfesa Ignatius Uduk

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) reshen jihar Akwa Ibom ta gurfanar da Farfesa Ignatius Uduk a gaban kotu.

Hukumar dai na tuhumar sa ne da bayyana sakamakon zaben karya yayin zaben Majalisar Dokokin jihar a 2019, lokacin yana Baturen Zabe a garin Afaha Ikot Ebak dake Karamar Hukumar Essien Udim ta jihar.

An gurfanar da shi ne bisa zarge-zargen aikata laifukan uku da suka hada da rubuta alkaluman karya a takardar shigar da sakamakon zabe, sanarwa da kuma wallafa sakamakon karya, sai yin karya a gaban Kotun Sauraron Kararrakin Zabe.

Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata laifukan, yayin da lauyansa, Samuel Ndah ya bukaci a ba da belin sa.

A nasa bangaren, jagoran lauyoyin INEC, Kpoobari Sigalo bukatar kotun ya yi kan kada ta kuskura ta bayar da belin wanda ake zargin.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Archibong Archibong dage sauraron karar ya yi har zuwa 14 ga watan Disamba 2020 domin yanke hukunci kan bukatar bayar da belin wanda ake tuhumar.