✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da alkalin bogi kan badakalar N10.6m a Kano

Ana zarginsa ne da yin sojan gona a matsayin alkali

An gurfanar da wani ma’aikacin gwamnati a gaban kotu, sannan aka aike da shi kurkuku saboda yin sojan gona a matsayin alkali, har ya karbi Naira miliyan 10.6 daga wani mutum.

Ana zargin Auwalu Muhammad, mai shekara 42 ne da yin sojan gona a matsayin alkalin kotun shari’ar Musulunci, kuma ya karbi kudin ne daga wani mai suna Jamilu Muhammad.

Kamar yadda takardar tuhuma ta kotu (FIR) ta nuna, wanda ake zargin, mazaunin unguwar Dorayi Babba ne da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

“Wani lokaci a watan Fabrairun 2022, mutumin ya gabatar da kansa a matsayin alkalin kotun shari’ar Musulunci sannan ya karbi Naira miliyan 10 da 650 daga wanda yake korafi, Jamilu Muhammad, da cewar zai sayar masa da wani fili,” in ji takardar.

Dan sanda mai gabatar da kara, Suleiman Sunusi, ya shaida wa kotun cewa laifukan da ake zargin mutumin sun saba da tanade-tanaden sassa na 312 da 302 da 309 da 179 na kundin Penal Code.

Laifukan dai sun hada da yin sojan gona cin amana da cuta kuma yin karya.

Sai dai bayan an karanta wa wanda ake tuhuma takardar a kotu, ya musanta aikata laifin.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki-Yola, ya ba da umarnin tsare wanda ake tuhumar zuwa ranar 28 ga watan Fabrairun 2023.