Da take tabbatar da hakan, Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Abuja, DSP Josephine Adeh, ta ce rundunar ta girke jami’an ne domin hana ’yan bandar siyasa da bata-gari sakat a lokacin taron.
- Shugaban ’Yan Sanda ya roke su kada su shiga yajin aiki
- Shugabancin APC: Sai dai Buhari ya yi wa dan takararsa kamfe —Fayemi
“Mun tura isassun jami’an tsaro domin sanya ido domin kada a samu saba doka da oda a ranar Asabar,” inji ta.
DSP Adeh, ta kuma yi kira ga manyan ’yan siyasa da su kasance masu bin doka, kada su tauye hakkin ’yan Najeriya.
Ta ce, “Za mu rika lura da abubuwan da ke faruwa da kuma samar da tsaro, baya ga girke jami’anmu a muhimman wurare.
“Jami’ai 1,815 da suka hada da masu binciken kwakwaf da masu dabaru na musamman domin maganin duk wata barazana da za ta iya tasowa,” inji ta.