Fadar White House ta Gwamantin Amurka ta girke jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda a Majalisar Dokokin kasar bayan masu zanga-zanga sun far wa Majalisar suna neman kutsawa ciki da karfin tsiya.
Daruruwan magoya bayan Shugaba Donald Trump sun mamaye Majalisar Dokokin kasar yayin da take shirye-shiryen tabbatar da nasarar Joe Biden a matsayin Zababben Shugaban Kasar.
- Sarakuna ke gayyato ’yan bingida —Gwamnan Neja
- Zanga-zanga: Magoya bayan Trump sun kutsa kai ginin majalisar Amurka
An yi gumurzu tsakanin jami’an tsaron Majalisar da masu tarzomar da suka yi ta farfasa abubuwa, yayin da ’yan Majalisar ke gudanar da zama.
Rahotanni sun ce an jikkata akalla mutum daya; hotuna sun nuna masu tarzomar kwakkwance a kasa yayin da jami’an tsaro ke kokarin sake karbe ikon ginin Majalisar na Capitol.
Tarzomar ta barke ne bayan Shugaba Trump ya yi kira ga magoya bayansa su yi maci zuwa Capitol.
Bayan tashin-tashinar, Fadar White House ta ce ta riga ta tura jami’an tsaron kasar domin kare Majalisar.
Mista Trump, wanda ya yi watsi da sakamakon zaben ya yi kira ga magoya bayan nasa da su koma gida, amma ya caccaki zaben.
Trump a cikin wani bidiyo ya bayyana cewar ya fahimci irin takaicin da suke ji, yayin da ya hakikance cewa shi ne ya ci zaben.
“An murde zaben, amma kada mu bari mu fada gadar zaren da mutanen nan suka shirya mana. Ku koma gida, ku koma cikin aminci,” inji shi.