‘Yan sanda sun gargadi masu fafutikar kafa kasar Oduduwa da kar su yi zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a yau ko a wasu ranakun.
Mataimakin Sifeto Janar na ’Yan sanda, mai kula da shiyyar Kudu maso Yamma, Leye Oyebade, ya ce umurnin ya fito daga Sifeto Janar na kasa, Muhammadu Adamu.
- Rashin Tsaro: An kama masu zanga-zanga 43 a Katsina
- Rashin Tsaro: An kama masu zanga-zanga 43 a Katsina
Oyelade ya ce zanga-zangar ka iya haifar da rikici musamman a daidai lokaci da Najeriya ke bikin cikarta shekara 60 da samun ’yancin kai.
Ya ce, ’yan sanda a shirye suke su tabbatar cewar wani mutum ko kungiya ba ta tayar da zaune tsaye ba a yankin.
Ya ce: “Iyaye kar su bari a yi amfani da ’ya’yansu wajen yin zanga-zangar.”
“Yau ne ranar bikin murnar samun ’yancin kai, bai kamata mu yi fada ba.”
“Babu dalilin da zai sa wani ya fito ya tayar mana da fitina.”
“Jami’an ‘yan sanda za su tabbatar da ganin cewa wani bai fito ya tayar hankalin mutane ba.”
“Wadanda kuma suka fito suna maganganun da ka iya tayar da zaune tsaye, su sani, muna da shaida a kan su don haka kar wani ya yi abinda zai kawo tashin hankali a kasar nan. ”