A yayin da damina ke kara kankama, Hukumar Wayar da kan Al’umma ta Kasa NOA ta gargadi manoma da su gu ji amfani da kwayoyi don kara kuzari a lokacin da suke aikin gona.
Daraktar hukumar a Jihar Gombe, Misis Adaline Waye Patari, ce ta yi kiran a lokacin da take zantawa da Wakilinmu a Gombe, inda ta ce amfani da kwayoyi masu kara kuzari yana da illa ga lafiyar su.
A cewarta, shan kwayoyi da ba likita ne ya rubuta ba yana da hatsari da zai iya haifar da matsalar kwakwalwa ta sa hauka.
” Zai fi kyau manoma su yi amfani da karfin jikinsu ba karfin kwaya ba domin shan kwaya ko wani abu mai sa kuzari yana nakasa mutum,” in ji Adaline.
Tace hukumar NOA da hadin guiwar wasu hukumomi da kungiyoyi sukan shirya taron fadakarwa kan guje wa shan kwayoyi barkatai a tsakanin matasa.
Ta ja kunnen manoma masu dabi’ar sanya kwaya a Nono ko wani abun sha suna bai wa yara masu yi musu aiki a gona don aiki tukuru ba tare da sun gaji ba.
“Idan kuna irin wannan hali ku bari ba halin kirki ba ne, cin zarafin yara ne domin yaran da ya kamata suna makaranta ne ake kai su gona don aikin karfi,” kamar yadda ta bayyana.
Daga nan sai ta kirayi masu ruwa tsaki da su dinga sa ido wajen kai ziyarar gani da ido a gonaki, da nufin l kama duk masu irin wannan hali saboda ya zama izina.