✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano sandar majalisa da aka sace

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta ce an gano sandar girma ta Majalisar Dattawa da wadansu ’yan daba suka sace a shekaranjiya Laraba. Haka kuma rundunar…

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta ce an gano sandar girma ta Majalisar Dattawa da wadansu ’yan daba suka sace a shekaranjiya Laraba.

Haka kuma rundunar ta ce an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen Majalisar Dokokin ta kasa.

Wannan bayani yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Kakakin Rundunar ta kasa SP Aremu Adeniran ya aike wa manema labaru.

Sanarwar ta ce an gano sandar ce a wani wuri da ke kusa da gadar kofar shiga birnin Abuja (City Gate).

Rundunar ta ce wadanda suka sace sandar sun jefar da ita ce sakamakon tsaurara matakan tsaro da ’yan sanda suka yi a Abuja. 

Hakan na zuwa ne bayan da Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo ya gana da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ike Ekweramadu. 

Sanata Ike Ekweramadu ya shaida wa manema labarai cewa ya je fadar gwamnati ce don yi wa Mataimakin Shugaban kasar karin bayani kan abin da ya faru a majalisar.

A shekaranjiya Laraba ce wadansu da ake zargin ’yan daba ne da ake zargin suna tare da Sanata Obie Omo-Agege suka kutsa zauren majalisar yayin da ake cikin zama suka dauke sandar.

An yi ta hargowa a majalisar a kokarin masu gadin wajen na su kwace sandar daga hannun mutanen su biyar, amma sai da suka tsere da ita daga majalisar mai dauke da jami’an tsaro 250 da suke aiki a lokacin.

A makon jiya ne aka dakatar da Sanata Omo-Agege daga majalisar kan nuna adawarsa da sauya fasalin zabe, kuma Kakakin Majalisar Sanata Sabi Abdullahi ya zarge shi da kawo ’yan dabar da suka sace sandar.

Sai dai wata sanarwa da ta fito daga ofishin Sanata Omo-Agege ta musanta cewa Sanatan ne ya kai ’yan dabar da suka sace sandar.

Sanarwar ta ce ya je majalisa ne kamar sauran abokan aikinsa don ya halarci zaman da ake yi a bisa shawarar tsarin shari’a da ya bi.

Rundunar ’yan sandan Najeiya ta kama Sanata Omo-Agege, a harabar majalisar bayan kammala zamanta, inda ta yi masa tambayoyi kafin ta sako shi.

Majalisar ta bai wa Sufeto Janar na ’Yan sanda da Shugaban Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), umarnin su nemo sandar a cikin awa 24, tare da kamo wadanda suka sace sandar.

Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya fadi a wata sanarwar cewa wannan al’amari cin amanar kasa ne, “Don hakan tamkar kokari ne na kawar da wani reshe na gwamnatin da karfin tuwo, don haka dole a dauki duk matakin da ya dace,” inji shi.

Sanata Sabi Aliyu ya ce wannan abu ci fuska ne ga majalisar, kuma tuni shugabannin majalisar suka yi Allah-wadai da hakan.