An bankado wasu matattu da ke kan karbar albashi da wasu masu cin albashi a bagas a ma’aikatar ilimi ta Jihar Imo.
Hukumar samar da ilimin bai daya ta Jihar Imo (IMSUBEB) ce ta gano akalla matattu 60 masu karbar albashi duk wata a ma’aikatar.
Binciken da hukumar ta gudanar ya kuma gano cewa akwai mutane da dama ’yan shekaru 60 da wadanda suka haura shekarun ritaya daga aiki kuma suke ci gaba da karbar albashi.
Akwai kuma fiye da ma’aikata 40 da ke karbar albashi a bagas ba tare da suna zuwa aiki ba.
Mukaddashin shugaban kwamitin binciken da Gwamna Hope Uzodinma ya kafa, Ukagba Stella, shi ne ya fayyace rahoyon a karshen mako.
Yayin karbar rahoton, Gwamna Uzodinma ya yaba wa kwazaon hukumar tare da karfafa gwiwar sauran ma’aikatu da hukumomin jihar da su yi koyi da ita domin tsaftace tsarin albashi a jihar.
Uzodinma ya ce gwamnatinsa ta tsaya tsayin-daka domin tabbatar da biyan albashin ma’aikata da masu karbar fansho a kan kari.
Ya bukaci dukkannin masu fuskantar matsalar samun albashi da su garzaya ofisoshin da suka dace domin mika bayanansu inda za a sanya kan sabon tsarin biyan albashi.
“Babu mahalukin da zai hana mu kammala zamanatar da tsarin albashin da aka faro. Abun takaici ne yadda masu adawa ke sukar kokarin, amma ba zan bari hakarsu ta cimma ruwa ba,” inji gwamnan.
A karshe ya nemi ’yan fansho da har yanzu ba su samu kudadensu ba da su kara hakuri a yayin da gwamnatin ke ci gaba da kokarin ganin an biya su hakkokinsu.