✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An gano matar da ta bace a gidan makwabci bayan shekara 11

Ta tare a gidan wani mutum da ta kamu da sonsa

Bayan shekara 11 an gano wata mata ’yar kasar Indiya, mai suna Sajitha da ta bar gidansu a shekarar 2010 kuma aka neme ta aka rasa.

A kwanan nan aka gano tana zaune a wani gida mai tazarar mita 500 kacal daga gidan iyayenta, inda take zaune da wani mutum da ta kamu da sonsa.

’Yan uwan Sajitha sun dade da mika wuya bayan bacewarta tun lokacin da ta bar gida a cikin shekarar 2010.

Sun rika tunanin ta mutu ko tana rayuwa a wani gari mai nisa, ba su taba tunanin tana cikin garin a kusa da su ba.

Sajitha mai shekara 18 a lokacin da ta bace, ta fita daga gidansu ne zuwa gidan masoyinta na sirri, wanda mutumin yankin ne da ya taba sanar da iyayenta game da soyayyarsu, amma iyayen ba su amince da shi ba.

Yadda suka gudanar da soyayyar asirce ba tare da sanin iyayensu ba tsawon shekara 10 labari ne da ya dace da wani shirin fim na Bollywood.

Budurwar ba ta bar wata alama ba lokacin da ta bar gidan iyayenta, kuma ba ta dauki wayar salula ba kuma ’yan sanda ba su iya yin wani taimako don gano ta ba.

Iyayenta ba su yi shakku game da soyayya da wani na kusa da su ba, kamar yadda mutum biyun suka bace ba daga kauyen Ayalur, a Kerala ba wanda ya ce komai.

An gano Sajitha ne kawai a farkon wannan wata bayan da wani mutumin garin mai suna Alinchubattil Rahman mai shekara 34 ba zato ba tsammani ya bace daga gidan danginsa wata uku da suka gabata, kuma danginsa suka sanar da ’yan sanda.

Dan uwansa Basheer ya same shi a gefen hanya wata rana, kuma ya samu nasarar binsa zuwa wani gida a kauyen da ke kusa da su, wanda a gidan da yake haya ne suke tare da Sajitha.

’Yan sanda sun gurfanar da ‘ma’auratan’ a gaban kotun yankin, wacce ta ba su damar zama tare bisa doka bayan sun ji labarinsu.

Sai dai abin mamaki su biyun sun fito ne daga addinai daban-daban kuma sun tabbatar cewa danginsu ba za su amince da soyayyarsu ba, don haka suka yanke shawarar kasancewa tare cikin sirri.

“Labarin nasu ba wani abu ba ne, amma mun dauki ‘ma’auratan’ zuwa gidan Rahman (inda Sajitha ta yi shekaru) kuma sun gaya mana yadda Sajitha ta zauna a asirce a daki daya tsawon wadannan shekarun,” kamar yadda jami’in ’yan sandan garin Nenmara, Deepa Kumar ya shaida wa kafar labarai ta Indian Express.