Wani masallaci ya bayyana, shekara 37 bayan nitsewarsa cikin wata madatsar ruwa da ke kasar Indiya
Masallacin, wanda ake yi masa lakabi da Masjid Noori ya nitse ne a madatsar ruwar Phulwaria da ke jihar Bihar a shekarar 1985 yanzu kuma da ruwan ya janye sai ya ga shi ya bayyana bai rushe ba.
- Kotun Indiya ta ba mabiya addinin Hindu damar yin bautarsu a masallaci
- Sun yi wata 8 suna gudanar da ofishin ’yan sanda na bogi a otel din Indiya
Mutanen yankin sun ce masallacin ya dade a wurin kafin a soma ginin madatsar ruwar, wanda hakan ta sa aka kwashe mutanen yankin tare da matsar da su zuwa wani wuri a 1979.
Bayan tashin jama’a an bar masallacin a yashe, a inda bayan gama aikin madatsar ruwar, ruwa ya mamaye yankin baki daya har ya shanye kan masallacin a inda nutse ba a ganin ko alamarsa.
Karancin ruwa da kuma fari da ake fama da shi a yankin a yanzu haka, ta sa madatsar ruwan ta kafe.
Wannan ya sa masallacin ya bayyana, kuma a tsaye kamar yadda yake a da, bai kuma rushe ba.
Bayyanar masallacin ta sa mutane na ta tururuwa cikin tabo da laka zuwa ganinsa suna kuma shiga cikinsa.
An kiyasta shekarun ginin masallacin 120 a duniya la’akari da tsari da kuma yanayin gininsa, a cewar masana.