Jami’an tsaron gabar tekun Girka sun ce sun gano gawarwaki 21 daga cikin kwale-kwalen bakin-haure biyu da suka nitse a farkon makon wannan makon.
A ranar Laraba jami’an suka ce an gano gawarwaki 20 a kusa da tsibirin Evia, kwana guda bayan wani jirgin ruwa da ake kyautata zaton yana dauke da mutane kusan 70 ya nutse a cikin tekun da ke cike da hadari.
- Shugaban PDP na Zamfara, Sani Ahmad, ya rasu
- Da kasashen Afirka za a soma rabon tallafin hatsin Ukraine – Erdoğan
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa (AFP) ya rawaito cewa, an kuma gano wata gawar a ranar Talata a wani hatsarin da ya auku a tsibirin Samos na kasar, inda wani jirgin ruwa daga gabar tekun Turkiyya ya kife dauke da mutane 12.
Sama da mutane 30 ne ake fargabar sun bace a hatsarin Evia, yayin da wasu bakwai suka bace a Samos.
Tun farko, jami’an tsaron gabar tekun sun tabbatar da mutuwar mutane 14 bayan aukuwar hatsarin.
Galibi, kasashen Girka da Italiya da Spaniya ne wuraren da bakin-haure musamman daga Afirka da Gabas ta Tsakiya ke zuwa don neman ingantacciyar rayuwa.