✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawarwakin mutum 2 a cikin tafki a Jigawa

Wannan mummunan lamari ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 a ranar Litinin,

Hukumar tsaro ta sibil difens (NSCDC) a Jigawa ta ce ta gano gawarwakin wasu mutum biyu a wani tafki da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu a jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar (PPRO), ASC Badaruddeen Tijjani, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Dutse.

Tijjani ya ce an tsamo gawar wani Abubakar Alhaji mai shekara 20 da Abubakar Abdullahi mai shekara 25 wadanda suka nutse ne ruwa a lokacin da suke tsallaka tafkin a hanyarsu ta zuwa kasuwa a ƙauyen Waza.

“Wannan mummunan lamari ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 a ranar Litinin.

“Babban jami’in NSCDC reshen Birnin Kudu, CSC Muhammad Garba ya tabbatar da cewa rundunar ta samu kiran gaggawa daga wasu mazauna unguwar da misalin ƙarfe 11:30.

“An tura mutanenmu yankin… domin aikin ceto.

“Tare da taimakon mazauna unguwar sun sami nasarar gano gawarwakin mutanen biyu da suka mutu bayan kimanin mintuna 48 ana aikin ceto,” in ji Tijjani.

Ya bayyana cewa an kai gawarwakin zuwa cibiyar lafiya ta Waza.

“Mun miƙa gawarwakin ga iyalansu kuma tuni aka binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,” in ji shi.