✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gano gawarwaki 5 a hatsarin jirgin ruwan Thailand

Jirgin ruwan yana dauke da mutum 105 a lokacin da hatsarin ya auku...

Masu aikin ceto sun sake gano mutum daya da ransa da kuma gawarwaki biyar na wadanda hatsarin jirgin ruwan yakin Thailand ya rutsa da su a karshen makon da ya gabata a Gabar Tekun kasar.

Sojojin ruwan kasar ne suka bayyana hakan, tare da cewa har yanzu akwai gomman mutanen da suka bace sakamakon nutsewar jirgin.

Rahotanni daga yankin sun ce jirgin yakin ya nutse ne a ranar Lahadi da daddare dauke da mutum 105.

Jami’an sun ce babu isassun rigunan kariya a cikin jirigin a lokacin da hatsarin ya auku, wanda hakan ya haifar da asarar rai da bacewar wasu da dama.

Hukumomin kasar sun ce kawo yanzu wadanda aka ceto da rasnu a hasatrin sun kai 76, an kuma gano gawarwaki biyar, yayin da ba ake neman mutum 24.