Masu aikin ceto sun sake gano mutum daya da ransa da kuma gawarwaki biyar na wadanda hatsarin jirgin ruwan yakin Thailand ya rutsa da su a karshen makon da ya gabata a Gabar Tekun kasar.
Sojojin ruwan kasar ne suka bayyana hakan, tare da cewa har yanzu akwai gomman mutanen da suka bace sakamakon nutsewar jirgin.
- Gwamnati ta jajanta wa fararen hula da jiragen yaki suka kashe a Zamfara
- Zargin ta’addanci: Kotu ta hana DSS kama Emefiele
Rahotanni daga yankin sun ce jirgin yakin ya nutse ne a ranar Lahadi da daddare dauke da mutum 105.
Jami’an sun ce babu isassun rigunan kariya a cikin jirigin a lokacin da hatsarin ya auku, wanda hakan ya haifar da asarar rai da bacewar wasu da dama.
Hukumomin kasar sun ce kawo yanzu wadanda aka ceto da rasnu a hasatrin sun kai 76, an kuma gano gawarwaki biyar, yayin da ba ake neman mutum 24.