An gano gawar wani shugaban Fulani da ya bace, Umar Ibrahim, a wata rijiya a unguwar Jokom da ke garin Mangu na Karamar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Marigayi Ibrahim shi ne Ciroma na gundumar Kumbun a Karamar Hukumar Mangu.
- Abba Gida-Gida ya naɗa sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Kano
- Dole mu dage wajen kare darajar bangaren shari’a — Alkalin Alkalai
Kakakin rundunar ‘Operation Safe Haven’ (OPSH) da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar, Kyaftin Oya James, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A halin da ake ciki, shugaban kungiyar Gan Allah Fulani (GAFDAN), ya bayyana cewa Ibrahim ya bace ne lokacin da ya fito daga asibiti a ranar Laraba don siyo wa matarsa abinci da ke garin Mangu amma bai dawo ba sai da yammacin ranar Lahadi da aka tsinto gawarsa a cikin rijiyar.
Shugaban kungiyar na jihar, Garba Abdullahi ya ce, “Ya ziyarci matarsa da ba ta lafiya da ke Mangu.
“Ranar Laraba misalin karfe 6 na yamma ya fita ya siyo mata abinci amma bai dawo ba.
“Bayan an shafe kwanaki hudu ana nemansa, an tsinci gawarsa a wata rijiya a kusa da asibitin.
“An tsinto gawar ce a gaban sojojin da ke aiki da rundunar ‘Operation Safe Haven’ da ke tabbatar da zaman lafiya a yankin.
“Sai dai duk da faruwar wannan lamari muna kira ga daukacin mambobinmu da su kwantar da hankalinsu, kada su dauki doka a hannunsu.
“Ya kamata mu ci gaba da zama masu bin doka. Hukumomin tsaro suna yin iya kokarinsu.
“Kiranmu ga jami’an tsaro shi ne kawai su kamo wadanda suka aikata wannan ta’asa domin a hukunta su.”