Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, ya ce an gano gawar akalla mutum 97 wadanda jirgin ruwa ya kife da su a garin Warrah da ke Karamar Hukumar Ngaski a Jihar.
Bagudu ya bayyana hakan ne a Birnin Kebbi yayin da yake karbar bakuncin ’yan Majalisar Wakilai da suka kai masa ziyarar jaje dangane da hatsarin.
- An sace Hakimi da matansa biyu a Neja
- ’Yar shekara 3 daga cikin daliban Islamiyya da aka sace ta rasu
A ranar 2 ga watan Yuni ce wani jirgi da ya taso daga Lokon Minna ya kife da fasinjojin cikinsa da suka hada da ’yan kasuwa da masu hakar ma’adanai wanda ya hallaka fiye da mutum 100.
Sakataren Gwamnatin Jihar wanda ya wakilci Gwamnan, Babale Umar-Yauri, ya ce tuni aka binne mutanen yayin da aka ceto mutum 22 da ransu.
Gwamna Bagudu ya yi godiya ga mambobin Majalisar Wakilan dangane da hangen nesansu na tabbatar da aminci a hanyoyin sufurin ruwa na Najeriya.
Ya kuma mika sakon son barka da fatan alheri na Gwamnatin Jihar zuwa ga Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, dangane da jajen da ya yi gami da kauna da kulawa da ya nuna wa al’ummar jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, tawargar ’yan Majalisar Wakilan ta kuma ziyarci Sarkin Yauri, Dokta Muhammadu Zayyanu Abdullahi.