A jiya Talata ne mazauna unguwar mil 5 da ke yankin Karamar Hukumar Birnin Kalaba, suka wayi gari cikin firgici da dimuwa sakamakon gano gawar mutum 15 maza da mata da aka watsar a magudanar ruwa da ke kan babbar hanyar shiga garin Kalaba.
Ganin yadda kudaje na kai kawo ne ya janyo hankalin mazauna yankin kan gawarwakin da aka yasar a magudanar ruwan.
Ana kyautata zaton riikici ne ya auku a wani wurin na daban sannan aka kwaso gawarwakin aka watsar a karkashin gadar da ruwan kwatami ke gudana.
Uwem Ekarika, wani mazaunin unguwar ya shaidawa Aminiya cewa, “Da safiyar Talata ce suka ga kudaje na yawo a wurin sai wari da hamami ke tashi shine ya sanya muka gano gawarwakin mutane ne aka yasar,” inji shi.
A yayin da babu tabbacin ko su waye suka kawo gawarwakin, sai dai wata majiyar ta shaidawa wakilinmu cewa, “an ji motsin tsayawar mota a wurin bayan dare ya raba amma babu tabbas ko daga ina aka kawo gawarwakin.”
Aminiya ta tuntubi DSP Irene Ugbo, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan kuros riba amma ba ta amsa kiran wayarta ba, inda har ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto duk wani yunkuri na jin ta bakin mahukunta ya ci tura.