✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gabatar da ƙudurin gyara masarautar Sarkin Musulmi a Sakkwato 

Idan gwamnatin jihar ta zartar da dokar za ta rage wa Sarkin Musulmi ikon naɗa muƙamai.

An gabatar da ƙudurin dokar yin gyara ga sashe na 76 na dokar ƙananan hukumomin a gaban Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato.

Wasu na ganin idan aka amince da dokar za ta rage ƙarfin iko na Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III.

Hakan ne ya janyo cece-kuce musamman a kafafen sada zumunta, wanda ta kai ga Mataimakin Shugaba Ƙasa, Kashim Shettima gargaɗin gwamnatin Sakkwato kan yunƙurin tsige Sarkin Musulmi.

Bayan gabatar da ƙudurin, an masa karatu na farko da na biyu, sannan aka miƙa shi ga kwamitin da ke lura da ƙananan hukumomi da masarautu a jihar.

Majalisar ta bai wa kwamitin kwana 10 domin tattaunwa tare da gabatar da rahotonsa ga majalisar.

Idan aka amince da dokar, za ta soke gyaran da aka yi na 2008, wanda ya bai wa Sarkin Musulmi, damar naɗa hakimai da iyayen ƙasa da kansa.

Idan gwamnatin jihar ta zartar da dokar, Sarkin Musulmin ba zai iya naɗa muƙamai ba har sai ya samu sahhalewar gwamnan jihar.

Aminiya ta ruwaito yadda gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya sauke wasu daga cikin hakimai da masu sarautar gargajiya a jihar a kwanakin baya.