✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fitar da mu ne saboda mafi yawan ’yan wasanmu sun ji rauni – Barista Ibrahim Gwadabe

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Babbar Kotun Kano  Barista Ibrahim Gwadabe ya ce gajiya ce da kuma rauni da wasu daga cikin ’yan…

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Babbar Kotun Kano  Barista Ibrahim Gwadabe ya ce gajiya ce da kuma rauni da wasu daga cikin ’yan wasansa  suka yi ne ya sanya kungiyar ba ta tabuka wani abin a-zo- a- gani ba a gasar cin kofin Babban Mai Shari;a na kasa (CJ Cup) da aka saba yi kowace shekara, bana kuma aka yi a Kalaba, Jihar Kuros Riba.

Barista Gwadabe, ya fadi haka ne zantawarsa da Aminiya a Kalaba jim kadan da kamala gasar.   Ya ce “tun lokacin da aka sanya gasar cin kofin CJ Cup kungiyarmu ba ta taba zama kashin baya ba kamar wannan lokaci domin kowace shekara mu ke zuwa na biyu muna kai wa wasan rarshe mu zo na biyu amma a bana sai ga shi a wasan kwata fainal aka fitar da mu”.

Da aka tambaye shi dalilin samun rashin nasarar da kungiyarsa ta yi  Barista Ibrahim Gwadabe ya ce “’yan wasanmu da yawa daga ciki sun samu rauni wanda hakan  ya haifar mana da koma-baya da kuma rashin samun nasara yayin da ragowar ’yan wasan kuma gajiya ce ta hana su tabuka komai”.

Dagan an ya ce za su koma gida su sake daura damara domin tunkarar gasa ta badi. Ya gode wa ’yan wasansa bisa kwazon da suka nuna yayin fafatawar sannan kuma jinjina wa shugabannin kungiyar da kuma Babbar Kotun Kano bisa goyon baya da kuma daukar dawainiyar wajen halartar gasar da ake yi a kowane bangare na kasar nan.